Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya za ta samar da yankunan raya tattalin arziki na musamman
2020-10-30 10:25:06        cri
Mahukunta a kasar Kenya, na shirin samar da damammaki na cin gajiya daga yankunan raya tattalin arziki na musamman ko SEZ a takaice, a wani mataki na bunkasa jawo jarin waje na kai tsaye, bayan an kai ga shawo kan cutar COVID-19.

Da yake tabbatar da wannan kuduri, cikin jawabin sa ga mahalarta taron yanar gizo game da harkokin cinikayya, babban sakatare a ma'aikatar masana'antu, cinikayya da bukasa sana'oi na kasar Francis Owino, ya ce gwamnatin Kenya na aiwatar da sauye sauye kan manufofi da dokokin gudanarwa, wanda za su karkato da hankulan masu zuba jari daga wajen kasar.

Mr. Owino ya kara da cewa, yankin raya tattalin arziki na musamman, na samar da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jarin waje, ta yadda za su iya samar da hajoji ga kasuwannin cikin kasar, da ma na kasashen waje. Jami'in ya ce, tuni gwamnati ta tsara samar da irin wadannan yankuna na SEZ guda 9 a sassan kasar daban daban.

Owino ya kara da cewa, wadannan yankuna na SEZ, za su kuma taimakawa kasar Kenya sarrafa tarin albarkatu da take da su, wadanda a baya ake fitarwa kafin sarrafa su. Ya kuma ce aikin kyautata darajar albarkatu a cikin gida, dama ce ta samarwa 'yan kasar karin guraben ayyukan yi, tare da rage dogaro ga hajojin da ake shigowa da su daga ketare, musamman wadanda za a iya samarwa a cikin kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China