Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Kenya za ta kara farfado da wuraren gwajin COVID-19 a kasar
2020-08-25 11:01:44        cri
Babban sakataren ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya, Rashid Aman, ya bayyana cewa, kasarsa za ta duba yiwuwar farfado da dakunan gwaje-gwaje da horas da ma'aikata, da samar da sinadaran gwaji, don kara karfin yin gwajin cutar COVID-19, sakamakon tarin matsalolin da suka hana rage yaduwar cutar.

Da yake karin haske yayin taron manema labarai a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar ta Kenya, Rashid Aman, ya ce, zamanantar da dakunan gwaje-gwaje dake sassa daban-daban na kasar, da kuma samar musu isassun ma'aikata, zai hanzarta gwajin cutar, cikin inganci da ma samun sakamako mai gamsarwa.

Ya kara da cewa, gwamnati tana inganta aikin gwajin cutar a sassan kasar, tare da tabbatar da cewa, an aika sakamakon ta hanyar na'ura. Sai dai ya yarda cewa, na'urorin gwajin da gwamnati ta samar a baya-bayan nan, sun fuskanci matsalar sinadaran gwajin cutar.

Aman, ya ce, ma'aikatarsa, tana hada kai da sassan da abin ya shafa, a wani mataki na inganta karfinsu na yin gwajin cutar COVID-19, a gabar da mahukuntan kasar ke kara kokarin dakile yaduwar cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China