Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsoffin Gonakin Gishiri A Sabon Zamanin Da Muke Ciki A Gundumar Markam Dake Jihar Tibet
2020-10-22 16:03:07        cri

Garin 'yan kabilar Naxi da ke gundumar Markam ta birnin Changdu na jihar Xizang ta kasar Sin yana kusa da kogin Lancang, wuri ne mai ni'ima da kyakyyawan muhalli. Haka kuma, garin na da albarkatun gishiri, gaba daya akwai gonakin gishiri 4155, da tabkunan gishiri sama da dari 3, da kuma rijiyoyin gishiri sama da 60 a wurin.

Wadannan tsoffin gonakin gishiri suna da tarihi sama da dubu daya, zuwa yanzu, an shafe sama da shekaru 1300 ana aikin samar da gishiri a wannan wuri. Fasahohin musamman da ake amfani da su wajen busar da gishiri da kuma kyakyyawan muhallan wannan wuri suna janyo hankulan masu yawon shakatawa. Cikin kowace shekara, ana samun mutane masu yawa da suke tafiya yawon shakatawa a garin, lamarin da ya ba da garin damar raya harkokin yawon shakatawa a garin Naxi.

Domin ba da gudummawar kawar da talauci, a shekarar 2017, aka kafa wani yankin yawon shakatawa na tsoffin gonakin gishiri da matsayinsa ya kai 5A, wanda ya janyo hankulan masu yawon shakatawa matuka. Jami'in kauyen Jiada na garin Naxi ya bayyana cewa, a halin yanzu, akwai gonakin gishiri sama da 3600 a kauyen, mutane daga gidaje kimanin 220 suna aikin samar da gishiri, ta wannan aiki kuma, suke samun galibin kudin shigarsu. Yanzu kuma, cikin kowace shekara akwai masu yawon shakatawa kimanin dubu 50 da suke zuwa yawon shakatawa a kauyen Jiada, lamarin da ya samar da karin kudaden shiga ga mazaunan wurin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China