Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda aka kawar da damuwar al'ummar garin Changshun wajen samun ruwan sha
2020-10-15 16:09:06        cri

Garin Changshun dake lardin Guizhou, gari ne da ya taba fama da matsalar karancin ruwa mai tsanani. Amma, yanzu, Wannan wuri cike yake da bishiyoyi masu launin kore shar, wanda ke da kyan-gani sosai.

A shekarar 2010, an yi bala'in fari mai tsanani a wannan gari, a lokacin, al'ummomin garin sun yi fama da matsalar karancin ruwa mai tsanani, ta yadda ba wanda zai iya mantawa da irin mawuyacin halin da suka taba gamuwa da shi ba.

Kauyen Daihua dake garin Changshun, daya ne daga cikin kauyuka mafiya fama da kangin talauci guda 20 na lardin Guizhou na kasar Sin. Kafin shekarar 2014, babu masana'anta da aka raya a wannan wuri. Amma a halin yanzu, an gina wurin tara ruwa a kauyen, an kuma shigar da ruwan famfo cikin gidajen al'ummomi. Haka kuma, ana kiwon aladu har dubu 50, da kifaye kilo dubu 300, da kuma kaji guda dubu 80, lamarin da ya sa, kauyen ya kasance mai samar da kayayyakin abinci ga duk fadin birnin Guiyang. Lalle wannan tsohon kauye ya samu bunkasuwar zamani.

An cimma wadannan sakamako ne bisa kokarin da gwamnatin wurin da al'umma suka yi cikin shekaru 10 da suka gabata, cikin wadannan shekarun baya, an zuba jari da ya kai sama da yuan biliyan 280 kan ayyukan ban ruwa, lamarin da ya sa, aka samar da ruwa har kyubik mita biliyan 12.37 a duk shekara a wurin. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China