Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta kaddamar da gangamin dakushe tasirin COVID-19 a Afirka
2020-08-21 09:49:50        cri

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta kaddamar da gangamin karfafa ayyukan dakushe tasirin cutar numfashi ta COVID-19 a sassan nahiyar Afirka. Fatan kungiyar shi ne kyautata tattalin arziki da rayuwar al'ummar nahiyar, yayin da ake kara saukaka matakan kulle.

A jiya Alhamis ne dai kungiyar ta AU, ta ce sabon shirin wanda aka yiwa lakabi da "Yakin da Afirka ke yi da COVID-19: Gangamin kare rayuka, tattalin arziki, da rayuwar al'umma", ya kunshi kare matafiya dake bin kan iyakokin kasashen nahiyar, yayin da kasashe ke kara bude harkokin tattalin arziki.

Hukumar AU mai lura da zamantakewar al'umma, da hukumar samar da makamashi da ababen more rayuwa, tare da cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta Afirka ko Africa CDC ne suka yi hadin gwiwar kaddamar da gangamin, yayin taron mako mako na bayyana yanayin da ake ciki game da cutar ta COVID-19 a Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China