Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu mutane 137 dauke da cutar COVID-19 da ba su nuna alamomin cutar ba a jihar Xinjiang
2020-10-26 14:26:10        cri

An samu mutane 137 dauke da cutar COVID-19 da ba su nuna alamomin cutar ba a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Yayin wani taron manema labarai, Gu Yingsu, mataimakin daraktan hukumar lafiya ta yankin, ya ce an samu dukkan mutanen ne a Kashgar dake kudancin jihar, bayan an tabbatar da wata matashiya mai shekaru 17 dake yankin Shufu na dauke da cutar, sai dai ba ta nuna alamunta ba.

Haka zalika, dukkan mutanen na da alaka da wata masana'anta dake Shufu, inda iyayen matashiyar ke aiki.

A cewar hukumar lafiyar, an killace matashiyar a wani asibiti dake Kashgar, domin nazartar yanayinta. Kawo yanzu, ba ta nuna alamomin cutar kamar na zazzabi ko tari ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China