Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe na fatan kara hadin kanta da kamfanonin kasar Sin ta fuskar kimiyya da fasaha ta zamani ciki har da Huawei
2020-09-06 16:55:54        cri
Kamfanin Huawei ya kaddamar da shirin samar da makoma a nan gaba a kasar Zimbabwe kwanan baya, dalibai 10 daga makarantu daban-daban zasu shiga wannan shiri na horar da fasahar sadarwa.

Mahalarta taron na bangaren Zimbabwe sun nuna cewa, kasar ta ci gajiya matuka a hadin kan da take yi da wasu kamfanonin sadarwa na kasar Sin, ciki har da kamfanin Huawei, suna fatan kara hadin kai da kamfanonin kasar Sin ta fuskar fasahar 5G.

Ministar yada labarai da farfaganda da rediyo na kasar Monica Mutsvangwa, ta ba da jawabi a taron cewa, tana godiya sosai ga taimakon da kamfanonin kasar Sin ciki har da Huawei suke bayarwa kasar a fannin sadarwa. Ban da wannan kuma, ministan sadarwa na kasar Jenfan Muswere, ya yabawa shirin da Huawei ya aiwatar, a ganinsa wannan shiri ya horar da kwararru da kasar ke matukar bukata.

An ce, an fara gudanar da wannan shirin ne tun daga shekarar 2015 a Zimbabwe, an rika zabar dalibai 10 a ko wace shekara don su karo ilmi a kasar Sin a fannin sadarwa da ma fasahar gudanar da harkokin kamfanonin dake da sassan daban-daban a duniya. Amma, a wannan karo za a gudanar da wannan shiri ta shafin Intanet sakamakon barkewar cutar COVID-19, wadannan dalibai 10 da aka zaba zasu shiga ajin Intanet a cibiyar horaswa dake Harare. (Amian Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China