Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe na son kara yawan audugar da take samarwa
2020-10-14 10:30:06        cri
Kasar Zimbabwe na duba yuwar samar da ton 400,000 na auduga a lokacin daminar bana, adadin da ya ninka wanda ta samar a bara har sau 5.

Ministan kula da aikin gona da filaye da ruwa na kasar, Anxious Masuka, ya kaddamar da wani shirin shugaban kasa na samar da kayayyakin noman auduga ga manoma, wanda a karkashinsa, iyalai 400,00 za su samu kayayyakin noma daga gwamnati.

Kayayyakin da gwamnati za ta bayar sun hada da irin auduga da taki da sinadari, da nufin ba manoman damar samar da yawan audugar da ake buri.

Ministan ya ce tuni gwamnati ta sayi kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 82 domin tallafawa manoman.

Auduga daya ne daga cikin amfanin gona dake samar da kudin shiga ga Zimbabwe, kana tana ba da gudunmmuwa ga ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar manomanta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China