Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta nuna rashin amincewa da sakin ruwa cikin madatsar GERD ba tare da cimma yarjejeniya ba
2020-06-18 11:03:11        cri

Mahukuntan kasar Sudan, sun yi watsi da shirin kasar Habasha, na sakin ruwa cikin madatsar nan ta "Grand Ethiopian Renaissance" wadda Habasha ta gina kan kogin Nilu, ba tare da cimma yarjejeniya kan hakan tsakanin Sudan da Masar da Habasha ba.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Khartoum, fadar mulkin Sudan, ministan albarkatun ruwa da noman rani na Sudan Yasir Abbas, ya ce kasar sa na shirin gabatar da matsayarta, ga fannin jagorancin siyasa na kasashen uku.

Ya ce Sudan na fatan cimma daidaito, ta yadda dukkanin kasashe masu ruwa da tsaki a wannan batu, za su iya cin gajiyar albarkatun ruwa ba tare da cutar da sauran kasashen ba.

Abbas ya kuma bayyana tattaunawar da kasashen 3 ke yi a matsayin mai cike da alfanu, wadda ga alama za a kaiwa ga cimma nasara, kafin ranar 1 ga watan Yuli dake tafe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China