Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin cika shekaru 70 da sojojin Sin suka taimaka wa Koriya ta Arewa wajen turjewa zaluncin Amurka
2020-10-23 10:32:00        cri

Yau Jumma'a, an yi bikin cika shekaru 70 da sojojin Sin suka taimaka wa Koriya ta Arewa wajen turjewa zaluncin Amurka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bikin, ya kuma ba da muhimmin jawabi.

Sojojin Sin sun shiga yakin Koriya ta Arewa domin turjewa zuluncin Amurka, da kuma kiyaye tsaron kasar Koriya ta Arewa da ma jamhuriyar jama'ar kasar Sin, sun kuma ba da babbar gudummawa wajen kiyaye zama lafiyar yankin da ma kasashen duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China