Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kulle kullen Amurka ba za su hana ci gaban salon kasa daya tsarin mulki biyu da Sin ke aiwatarwa ba in ji wani jamiin HK
2020-10-16 12:47:07        cri
Kakakin ofishin kwamishinan ma'aikatar wajen Sin a yankin musamman na Hong Kong, ya yi watsi da wani rahoto da Amurka ta fitar, game da abun da ta kira da "Dokar 'yancin Hong Kong ".

Jami'in ya ce, rahoton na Amurka ya fito karara, yana sukar dokokin gwamnatin kasar Sin masu nasaba da tsaron kasa a HK, tare da kare matakin sanyawa wasu jami'an Sin takunkumi, da kuma tsoma baki cikin harkokin HK, duk da kasancewar su harkoki ne na cikin gidan kasar Sin.

Ya ce dokokin tsaron kasa na HK, sun kara kyautata yanayin tsaron al'ummar yankin na musamman, sun kuma dakile ayyukan 'yan a-ware masu samun 'yancin kan yankin HK. Kana sun magance yanayi na tashe tashen hankula da masu tada kayar baya ke haifarwa.

Yanzu haka dai HK ya dauki wani sabon salo na magance tashe tashen hankula, an kuma bude sabon shafi na aiwatar da manufar kasa daya tsarin mulki biyu. Har ila yau, dokokin tsaron kasar da aka kafa, na shafar wasu 'yan tsiraru ne masu tsattsauran ra'ayin kin jinin Sin, masu barazana ga tsaron kasar. A hannu guda kuma, dokokin na ba da kariya ga mafiya rinjaye dake bin doka da oda, ciki har da baki 'yan kasashen waje dake zaune a HK. Hakan a cewar jami'in, ya samar da zarafi na kare hakkokin al'ummar HK bisa doka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China