Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Amurka ta dakatar da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin bisa hujjar batun Tibet
2020-10-20 19:54:05        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana yau Talata a nan birnin Beijing cewa, kamata ya yi kasar Amurka ta dakatar da yin amfani da batun Tibet, tana tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da hana ci gaba da kwanciyar hankali a yankin Tibet, sa'an nan kuma, ta daina goyon bayan duk wani yunkuri na masu rajin neman 'yancin kan Tibet, don haifar wa kasar Sin da baraka. Ya ce kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba, domin kiyaye hakkokinta.

An ruwaito cewa, 'yan adawar Tibet da ke zaune a ketare sun sanar a ranar 16 ga watan nan cewa, a wannan rana, jagoransu Lobsang Sangay, ya gana da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, kuma sabon jami'in kula da harkokin Tibet a ma'aikatar harkokin wajen Amurka Robert A. Destro. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China