Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in kasar Sin ya rarraba dabarun kasar Sin na kawar da talauci ga majalisar kare hakkin bil Adama na MDD
2020-10-09 13:51:12        cri
An kira dandalin al'umma na shekarar 2020 na majalisar kare hakkin bil Adama na MDD a jiya Alhamis. Mataimakin direkta ofishin kula da harkokin kawar da kangin talauci na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Chen Zhigang ya ba da jawabi ta bidiyo, don rarraba dabarun kasar Sin a wannan fanni.

Chen ya yi nuni da cewa, jami'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da gwamnatin Sin, na mai da hakkin rayuwar jama'a, da samun bunkasuwa a gaban komai, kuma tana dukufa kan aikin kawar da kangin talauci, da tabbatar da hakkin bil Adama. Daga shekarar 2012 zuwa 2019, yawan matalauta na kasar Sin ya ragu zuwa miliyan 5.51, daga miliyan 98.99. Ban da wannan kuma, manyan ababen more rayuwa, da karfin ba da hidima a wuraren dake fama da talauci na kara samun ingantuwa, matakin da ya sa ake rika kyautata halin da matalauta suke ciki. Ya kuma kara da cewa, Sin na da cikakken tsarin kawar da kangin talauci bisa halin da take ciki, kuma tana da nagartattun manufofi a wannan fanni.

Kaza lika, Chen ya bayyana dabaru masu kyau da Sin take aiwatarwa bisa wasu hotuna, da alkaluma, da abubuwan misali. Ya ce ya zuwa yanzu, Sin tana magance cutar COVID-19 a mataki-mataki, kuma ba shakka za ta kai ga cimma nasarar kawar da kangin talauci a duk fadin kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China