Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sauye-sauyen Gidaje A Birnin Ulanhot A Jihar Mongolia Ta Gida
2020-10-21 21:20:31        cri
Wang Chunlu, wani mazauni birnin Ulanhot na jihar Mongolia ta Gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin ne. Tun lokacin kuruciyarsa, ya rika daukar hotunan abubuwan da suka faru ga iyalinsa. Wasu littattafan hotunan da ya dauka sun nuna sauye-sauyen da aka samu ga iyalinsa cikin shekaru da dama da suka wuce, inda sauyawar yanayin gidajensu ta fi burge shi.

A shekarar 1978, Wang Chunlu, wanda soja a wancan lokaci, ya yi aure. Bayan bikin auren, ya koma rundunar soja, yayin da matarsa ta ci gaba da rayuwa tare da mahaifanta. A shekarar 1983, Wang Chunlu ya yi ritaya daga soja, shi da iyalinsa suka yi hayar wani tsohon gida, wanda fadinsa bai wuce murabba'in mita 20 ba. Sakamakon ci gaban kasar Sin, ya sa a shekarar bara, iyalin Wang Chunlu suka koma wani sabon gida mai fadin murabba'in mita 130 ko fiye da haka, inda kuma ake amfani da na'urar daukar mutane a benaye wato lift.

Baya ga iyalin Wang Chunlu, sakamakon aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare a kasar Sin, ya sa an samu manyan sauye-sauye a birnin na Ulanhot ta fuskar gidaje. Inda a yanzu matsakaicin fadin gidan ko wane mazauni birnin ya kai murabba'in mita 27.8, a maimakon mita 3.8 a shekarar 1980. Baya ga samun gidaje masu kyau da mazauna birnin suka yi, gidajen sun kuma kasance masu inganci sosai. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China