2020-10-20 12:06:23 cri |
Akwai sanyi sosai a kauyen Dabeishan, wannan ya sa ba a iya noma hatsi sosai a wurin. Gao Xiuhu ya koyi dabarun shuka Lingzhi, a don haka ya ce yanayin kauyen ya dace da shuka Lingzhi, zai kuma kara samun kudin shiga da kawar da talauci.
A bisa tallafin kudi da goyon bayan da ya samu daga hukumomin kula da nakasassu da kungiyoyin kimiyya da fasaha na garin Jingyu na birnin Baishan, Gao Xiuhu ya yi hayar wani fili dake kauyen a shekarar 2012, inda fara shuka Lingzhi.
A yayin da yake kokarin shuka Lingzhi, garin Jingyu ya gabatar da wasu manufofi da matakan yaki da talauci da goyon bayan sana'o'in musamman. Don haka, Gao Xiuhu ya samu kudin shiga fiye da kudin Sin Yuan dubu 20 a wannan shekara, wanda ya kara imanin ci gaba da raya sha'aninsa. Bayan wasu shekaru, ya kara fadin filayen da yake shuka Lingzhi, don kawar da talauci.
Sannu a hankali, sha'anin Gao Xiuhu ya samu ci gaba sosai. A shekarar 2013, ya kafa wata kamfani don jagorantar mazauna kauyen inda suke aiki tare da shi. Ya kuma samar da ayyukan yi ga mazaunen kauyen, da kafa sansanin nakasassu na yaki da talauci, da yin rajista da kafa kamfaninsa da sauransu. A shekarar 2020, yawan kudin da kamfaninsa ya samu daga sayar da Lingzhi ya kai Yuan kimanin miliyan 4.
Haka kuma, Gao Xiuhu ya horar da fasahohinsa na yin shuke-shuke a dutsen Changbaishan a dukkan lardin Jilin, yawan mutanen da ya horar da su ya zarce dubu daya. Ya ce, wannan tamkar shirin ba da iri ne, hakan zai taimaka wajen kawar da talauci tare. (Zainab Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China