Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kamata ya yi Amurka ta mutunta matsayin da Sin take dauka don ingiza maido da dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata
2020-09-03 11:23:50        cri

Mataimakin darektan kwamiti mai kula da harkokin waje, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Kong Quan, ya bayyana a kwanan baya cewa, a baya bayan nan, dangantakar kasashen Sin da Amurka na fuskantar kalubale, kuma ya dace Amurka ta mutunta matsayin da Sin take dauka, don kaucewar fito na fito da juna, da ma kokarin daidaita bambancin ra'ayi, har ma da habaka hadin kai don ingiza maido da dangantakar kasashen biyu.

Kwanan baya, wasu 'yan siyasar Amurka sun rika yada jita-jita, cewa wai Amurka ta ci tura kan manufar da ta dauka kan kasar Sin, kuma Amurka ta yi hasara, da dai sauransu, har sun rika kira da a dauki matakin cacar baka.

Game da hakan, Kong Quan ya shedawa manema labarai cewa, batun zargin wai Amurka ta yi hasara, na da alaka ne da rarar kudin da Sin take samu a fannin cinikayyar ta da Amurka. To amma kuma a hakika, Amurka ma ta taba samun rarar kudi yayin hada hadar cinikayya da Sin a dogon lokaci, kuma yawancin riba mai nasaba da wannan bangare, kamfanonin Amurka dake kasar Sin ne suke samu. Kuma ko kadan, kasar Sin ba ta cin zarafin Amurka a wannan fanni.

A cewarsa, dangantakar kasashen biyu, na bunkasa bisa tushen amincewa, da kuma mutunta tsare-tsaren mulkin kasa, masu bambanci da mutunta muradun juna, tun lokacin da suka kafa dangantakarsu. Ta wannan hanya za a iya tabbatar da bunkasuwar dangantakarsu, da ma hadin kansu da cin moriya tare.

Kong ya kara da cewa, wasu masanan Amurka, suna yin kira da a mai da hankali kan illar da rikicin dangantar kasashen biyu ke kawowa Amurka, kuma a ganinsu, ya kamata Amurka ta zura ido kan muradun kasa da kasa, da ma makomar bil Adama baki daya, don hadin kai da mu'ammala da kasar Sin yadda ya kamata, ta yadda za a ciyar da bunkasuwar duniya cikin lumana da wadata gaba cikin hadin kai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China