2020-09-05 16:17:45 cri |
Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiyar kungiyar tarayyar Afrika AU, a sanarwar da ta fitar ranar Juma'a ta ce, yawan mutanen da annobar ta yi ajalinsu a nahiyar ya karu zuwa 30,596. Sai dai, yawan mutanen da suka murmure daga cutar COVID-19 a Afrika ya kai 1,015,865, ya zuwa tsakiyar ranar Juma'a.
Jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kasance kashi 5 bisa 100 na yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya baki daya, in ji hukumar.
Africa CDC ta ce, kasashen Afrika 9 su ne ke da kashi 81 bisa 100 na yawan sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19 a makon da ya gabata a nahiyar, wanda ya hada da Afrika ta kudu mai kashi 27%, Habasha na da kashi 17%, Morocco kashi 16%, Libya kashi 5%, Algeria kashi 4%, sai kasashen Kenya, Najeriya, Namibia da Masar suna da kashi 3% kowannensu. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China