Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkawari kaya ne
2020-10-17 18:37:57        cri

A kwanakin nan, jakadun kasashen nahiyar Afirka da wakilan wasu cibiyoyin Afirka a kasar Sin 51, sun ziyarci babbar cibiyar gwaje gwaje da binciken rigakafin cututtuka ta kamfanin Sinopharm CNGB na Sin. A ziyararsu a cibiyar, jami'an jakadancin sun ganewa idanunsu yadda ake nazari da kuma samar da alluran rigakafin cutar Covid-19, da ma dakin gwaji na zamani.

A gun taron musayar ra'ayoyi da aka gudanar bayan ziyarar, jakadan jamhuriyar Nijer a kasar Sin, Inoussa Moustapha ya ce, kasar Sin ba ta tsirar da kanta kadai ba a lokacin da take kokarin yaki da cutar Covid-19, a maimakon hakan, ta hada gwiwa da kawayenta na Afirka. Kasar Sin tare da hukumomin kasa da kasa da abin ya shafa sun samar da babbar gudummawa ga kokarin da al'ummomin duniya ke yi na yaki da annobar.

Winnie N. Chibesakunda, a matsayinta na jakadiyar kasar Zambia a kasar Sin, ta bayyana cewa, ingantaccen tushen nazarin kimiyya da fasaha da ma kwarewarta wajen samar da alluran rigakafi, duk sun aza harsashi ga kasar ta Sin wajen samar da alluran rigakafin cutar Covid-19 masu inganci.

Yanzu haka, kasar Sin tana kan gaba wajen nazarin rigakafin cutar Covid-19. Ya zuwa karshen watan Satumba da ya wuce, akwai nau'o'in alluran rigakafin cutar 11 da aka gudanar da gwaje-gwaje a kansu, a yayin da aka shiga mataki na uku na gwaje-gwajen a kan wasu nau'o'i hudu daga cikinsu.

A gun taron koli na musamman na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wajen yaki da annobar Covid-19 da ya gudana a watan Yuni, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a jawabinsa cewa, "Bayan kasar Sin ta kammala nazarin rigakafin cutar Covid-19 tare da samar da shi, tana son baiwa kasashen Afirka fifiko wajen amfani da su." Sai kuma a kwanan baya, kasar Sin ta kulla yarjejeniya da kungiyar samar da allurar rigakafin cututtuka ta kasa da kasa, tare da shiga shirin COVAX a hukumance, domin ganin an rarraba rigakafin cikin daidaito da adalci da tabbatar da cewa, za ta samarwa kasashe maso tasowa. A game da wannan, jakadan tarayyar Nijeriya a kasar Sin Baba Ahmad Jidda ya ce, "muna kira ga kasar Sin ta samu wannan magani, domin mu kasashen Afirka mu samu mu ba jama'armu. Yawancin jama'armu ba su da karfi, kuma ba su da hali, sabo da haka muna neman taimakon kasar Sin, kuma muna kira muna addu'ar su samu da wuri, don mu samu zaman lafiya."

A bana ake cika shekaru 20 da kafa dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Karkashin tsarin dandalin, hadin gwiwar sassan biyu ta fannin kiwon lafiya ma ya samu saurin ci gaba. Bayan barkewar annobar a bana, Sin da kasashen Afirka sun rika taimakon juna da kuma tallafawa juna. A yayin da kasar Sin ke cikin mawuyacin hali, shugabannin kasashen Afirka sama da 50 sun bayyana goyon bayansu tare da samar da kayayyakin tallafi ga kasar Sin. Bayan da annobar ta fara bulla a kasashen Afirka, gwamnatin kasar Sin da kamfanoninta sun kuma samar da gudummawar kayayyakin jinya ga kasashen Afirka sama da 50, tare da tura kwararrun likitoci kimanin 148 zuwa wasu kasashen Afirka 11.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, "Sin da kasashen Afirka makomarsu daya ce." Abin haka yake, yadda Sin da kasashen Afirka suke tafiya kafada da kafada a yayin da suke fuskantar babbar matsalar lafiyar al'umma, ya bayyana ainihin ma'anar makomar bai daya ta sassan biyu.

Mukaddashin jakadan kasar Habasha a kasar Sin Genet Teshome Jirru ya ce, "Tarihin cudanyar Sin da kasashen Afirka ya shaida cewa, kasar Sin tana cika alkawuran da ta dauka a kullum." Alkawari kaya ne, a wannan karo ma, kasar Sin za ta cika alkawarin da ta dauka, don taimaka wa kasashen Afirka cimma nasarar yakar cutar Covid-19.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China