![]() |
|
2020-05-24 21:20:09 cri |
A yayin da yake tsokaci kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, Wang Yi ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka 'yan uwa ne dake da buri da makoma iri daya, a lokacin da kasar Sin take fama da matsalar cutar numfashi ta COVID-19, shugabannin kasashen Afirka sama da guda 50 sun aika sako ga kasar Sin, inda suka nunawa kasar Sin cikakken goyon baya, sun kuma bada taimako ga kasar Sin. Shi yasa, a halin yanzu, kasar Sin zata ci gaba da taimakawa Afirka a yaki da cutar Covid-19, tare da rage basusukan da ake binsu.
Ya kuma kara da cewa, a yayin da ake tsaka da yaki da cutar Covid-19, Sin da kasashen Afirka zasu ci gaba da hada kai da juna, kuma kasar Sin zata ci gaba da samar da gudummawarta ga kasashen Afirka, zata kuma baiwa kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa fifiko wajen samar musu gudummawar kayayyakin jinya, tana kuma shirin tura sabon ayarin jami'an lafiya zuwa Afirka.
Banda wannan kuma, Wang Yi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin zata yi kokarin aiwatar da shawarar kungiyar G20 ta "saukaka basusukan da ake bin kasashen Afirka", don saukaka wahalar da suke fuskanta ta fannin basuka. Tana kuma shirin kara samar da gudummawa ga kasashen Afirka da suke matukar fuskantar matsala, don taimaka musu haye wahalhalun.
Ko shakka babu, dadaddiyar zumuntar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka zata jure jarrabawar da suke fuskantar, kana sassan biyu zasu kafa kyakkyawar makoma yayin da suke dukufa wajen neman ci gaba cikin hadin gwiwa. (Maryam Yang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China