Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin Gwiwar Yaki Da Cutar COVID-19, An Bude Sabon Shafi Na Zumuncin Sin Da Afirka
2020-06-20 17:10:08        cri

A daren ranar 17 ga wata, an yi taron kolin musamman tsakanin shugabannin Sin da Afirka kan hadin gwiwar yaki da cutar numfashi ta COVID-19. A yayin taron, bangarorin da abin ya shafa sun yi musayar ra'ayoyi kan harkokin goyon bayan kasashen Afirka wajen yaki da annobar, da kuma inganta hadin gwiwar yaki da annobar a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da kuma tsakanin kasa da kasa, inda suka cimma matsayi daya kan wasu muhimman batutuwa. An kuma fitar da sanarwar hadin gwiwa cikin taron, inda aka sanar da matsayi daya da Sin da Afirka suka cimma kan wasu manyan batutuwa, da sanar wa kasa da kasa hadin gwiwa mai karfi dake tsakanin Sin da Afirka a wannan lokaci na musamman.

 

 

Kasar Sin da kasashen Afirka sun zama 'yan uwa, wadanda suke da buri iri daya. A lokacin da kasar Sin take fama da matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, kasashen Afirka sun bata babban goyon baya, kasar Sin ba za ta manta da wannan ba. Kana, bayan barkewar annobar a kasashen Afirka, kasar Sin ta zama kasa ta farko da ta samar wa kasashen Afirka taimakon da suke bukata, lalle Sin da Afirka suna goyon bayan juna a ko da yaushe. Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wajen yaki da annobar ya bayyana ma'anar dunkulewar Sin da Afirka sosai, lamarin da ya zama abin koyi ga kasa da kasa, ta fuskar hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19.

Annobar cutar numfashi ta COVID-19, abokiyar gaba ce ta dukkanin bil Adama, babu wata kasar da za ta iya cimma nasarar yaki da cutar ita kadai. Kuma ba za mu iya cimma nasarar yaki da wannan cuta ba, in ba mu kawar da ra'ayin siyasantar da batun annoba, da kuma ra'ayin wariyar launin fata ba.

Tabbas ne, za mu cimma nasarar yaki da wannan cuta. zaman rayuwar al'ummomin kasashen Sin da Afirka zai samu kyautatuwa kamar yadda ake fata. Nasarar da aka cimma wajen gudanar da wannan taro, za ta daga dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi. Kana, aiwatar da sakamakon taron yadda ya kamata, da ba da gudummawa ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar, za su iya karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, kuma, tabbas ne, lamarin zai kara tallafawa al'ummomin Sin da Afirka, har ma da al'ummomin kasa da kasa bai daya. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China