Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen Da Suke Rayuwa A Tsauni Mai Sanyi A Kasar Sin Sun Samu Ruwan Sha Daga Rijiyoyi
2020-10-09 11:01:58        cri

A saboda dalilai na yanayin kasa, mutanen gundumar Baokang na lardin Hubei su kan samu ruwan da za su sha ne daga ruwan sama ko ruwan kankara daga zuriya zuwa zuriya. A shekarar 2017, a kauyen Zhaojiashan na garin Maliang dake gundumar Baokong an haka rijiya ta farko duk da wahalhalu da dama da ake fuskanta, matakin da ya kawo karshen matsalar karancin ruwan sha mai tsabta da wurin ke fuskanta, hakan ya sa mazauna wurin suna da damar raya sha'anoninsu ta yadda za su fita daga kangin talauci da samun zaman rayuwa mai wadata.

Wang Qiang na farin ciki matuka, saboda isasshen ruwan sha mai tsabta ya ba shi damar raya sha'anin kiwon dabobbi. A cikin shekaru 2 kacal da suka gabata, ya habaka sha'aninsa har ya samu kudin shiga fiye da RMB Yuan dubban daruruwa a shekarar bara.

Saboda ganin haka, gundumar ta yada fasahar haka rijiya ta kauyen Zhaojiashan zuwa sauran wurare, an haka rijiyoyi 10 masu zurfi a garuruwa 5, matakin da ya samarwa mutane kimanin dubu 33 ruwan sha mai tsabta. Yanzu, mazaunan kauyen Zhaojiashan, wadanda a baya ke shan ruwan dake kwarara daga tsauni, yanzu suna da ruwan sha mai tsabta, kuma sun fita daga kangin talauci, suna kuma rayuwa cikin nishadi, ba tare da damuwa ta rashin abinci, ko tufafi da ruwa ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China