2020-09-29 10:59:58 cri |
Tun lokacin da aka gabatar da babban shiri raya kasa na 13, mai cin shekaru biyar-biyar, karuwar yawan makamashin da ba ya bukatar gas ko kwal da Sin ta yi amfani da shi ta kai kashi 40% na karuwar dukkan makamashi da aka yi amfani da su, adadin da ya karu da kashi 14% bisa na lokacin babban shirin na 12.
Irin wadannan makamashi na kunshe da makamashin da ake iya sake amfani da shi, da wutar lantarki da aka samar bisa karfin nukiliya, wadanda suka kasance muhimman makamashi maras gurbata muhalli. A lokacin aiwatar da babban shirin raya kasa na 13, ana gaggauta fitar da sabbin makamashi, da makamashin da ake iya sabuntawa, ta yadda ake samun damar kyautata tsarin makamashi na kasar. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China