2020-09-28 11:27:08 cri |
Rahotanni na cewa, sha'anin yawon shakatawa na kasar Sin ya samu farfadowa, inda a cikin rubi'i na 3 na shekarar bana, yawan mutane, da wuraren yawon shakatawa rukunin "A" na kasar suka karba, ya karu har ya kai kashi 70%, bisa na makamancin lokaci na bara, inda wasu wurare kuma, suka yi daidai da na makamancin lokaci na bara.
An ce, yawan mutanen da suka dawo bakin aiki a kamfanoni masu ba da hidima a wannan sha'ani, ya kai kashi fiye da 75% bisa matakan da aka dauka, kana yawon shakatawa na rukunonin mutane ya samu farfadowa da kashi 40%, bisa makamancin lokaci na bara. A daya bangaren kuma, otel-otel masu inganci 9,421 sun farfado da aikinsu, kuma yawan ma'aikatan da suka koma bakin aikinsu a wannan fanni ya kai kashi 91%.
Ya zuwa yanzu, wuraren bude ido rukunonin "5A" guda 280 a kasar Sin, sun gudanar da tsarin yin odar ziyara kafin lokaci, wanda ya zama mataki mafi dacewa da ake dauka, wajen gudanar da aikin yawon shakatawa. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China