Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dandalin FOCAC ya kara bunkasa alakar Sin da Afirka
2020-10-14 17:13:17        cri

Tafiya sannu-sannu aka ce kwana nesa, yanzu haka dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC ya cika shekaru 20 da kafuwa, dandalin dake zama babbar alamar hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.

Daga shekarar 2000 da wanzuwar wannan dandali zuwa yanzu, bangarorin biyu sun tsaya tsayin daka wajen raya al'ummominsu, da dukufa wajen inganta dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu. Haka kuma, sakamakon da aka cimma a tarukan FOCAC sun taimaka matuka ga al'ummomin Sin da Afirka.

Ga mai bibiyar nasarorin dandalin na FOCAC, zai fahimci cewa, Sin da Afirka sun cimma matsayi daya wajen karfafa hadewar al'ummominsu waje guda, lamarin da ya taimaka ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

A karkashin wannan dandalin ne, kasar Sin ta fito da jerin matakan taimakawa Afirka a fannonin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, da suka hada da layin dogo, da hanyoyin mota, da filayen jiragen sama, da tashoshin jiragen ruwa, da filayen wasanni na zamani, da musayar kwararru, aikin gona, al'adu da makamantnsu.

A yayin da sassan biyu wato, Sin da Afirka ke kara bunkasa alakar dake tsakaninsu don samun moriyar juna, a hannu guda kuma wasu kasashen yammacin duniya, na yiwa wannan kyakkyawar dangantaka bahaguwar fahimta, har ma a wasu lokuta suke neman bata dangantakar da ke kara bunkasa a dukkan fannoni.

Bayan bullar cutar COVID-19, wadda ta kasance babbar matsalar da ta shafi daukacin bil Adama, da haddasa babbar illa ga tattalin arzikin duniya, karkashin hadin gwiwar Sin da Afirka a fannoni daban-daban, sassa biyu yin hadin gwiwa domin fuskantar wannan kalubale tare, ta yadda hadin gwiwarsu ta kasance abin misali ta fuskar raya hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban don cimma moriyar juna, da ba da gudummawa wajen nuna adalci yayin tafiyar da harkokin duniya.

A shekara mai zuwa ne, za a shirya taron dandalin FOCAC na gaba a kasar Senegal, taron da masana suka yi imanin cewa, zai taimakawa Sin da Afirka wajen cimma burinsu na bai daya, tare da bayyana muhimmancin cudanyar bangarori daban-daban da kullum kasar Sin ke yayata bukatar dorewarsa a duniya. Hannu daya, aka ce ba ya Daukar Jinka. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China