Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsin lambar Amurka babu abun da zai haifar sai ma karawa Sin kwarjini
2020-10-13 17:35:42        cri

Shugaban tawagar kasar Sin, kuma mataimakin wakilin dindindin a MDD Geng Shuang, ya yi watsi da kiran da Amurka ta yiwa kasar Sin, na shiga wata yarjejeniya mai nasaba da kwance damarar makaman nukiliya tsakanin Amurka da Sin da Rasha yana mai cewa babu adalci a bukatar da Amurka ta bijiro da ita.

Amurka ta dade tana zarge-zarge marasa tushe game da makaman Sin tare da matsawa mata ta shiga tattaunawar da take yi kan kwance damarar makamai da Rasha, sai dai ta gaza bayyana yadda ta tsara tafiyar da tattaunawar ko yarjejeniya. Ta yaya ma za a yi wata kasa ta shiga yarjejeniya ido rufe? Baya ga haka, mene ne dalilin matsawa kasar da ba ta da yawan makaman da ita Amurkar ke da su, bayan tana da kawayen da yawan nasu ya zarge na Sin?

A cewar kungiyar dake rajin wayar da kan al'umma kan manufofin kwance damarar makamai dake da mazauni a birnin Washington na Amurka, akwai gibi mai yawa tsakanin yawan makaman da Sin take da su da na Amurka da Rasha, don na Sin bai kai kaso 50 na yawan wadanda suka mallaka ba.

Kasar Sin ta sha nanata matsayarta na cewa ba ta sha'awar shiga irin wannan yarjejeniya da Amurka da Rasha, wadda Amurkar ta gabatar, wadda ta bayyana a matsayin wani yunkuri,na kawar da hankalin duniya daga muhimman al'amura, da suka hada da bukatar da aka dade ana mika mata, na kwance damarar makamanta na nukiliya, yayin da take kara daukar matakan neman samun fifiko kan sauran kasashe a wannan fanni.

Kasar Sin ta sha nanata matsayarta na adawa da takarar mallakar irin wadannan makamai da kira da a aiwatar da yarjejeniyoyin kwance damarar makamai da aka cimma, kana tana goyon bayan hadin gwiwa a fannin tsaron duniya. Ai gudunmawar kasar Sin a fannoni daban-daban ciki har da tsaro, da kwance damarar makamai abu ne da duniya ta shaida.

Bugu da kari, kasar Sin ta kasance mai bin tsarin amfani da makaman nukiliya domin tsaron kai, sannan tana tara su ne bisa matsakaicin matakin da aka tanada, da nufin tsaron kasa kadai. Sannan ba ta da burin amfani da su wajen mamaya ko danniya.

Duba da babban gibin dake akwai tsakanin Amurka da kawayenta da kuma Sin a wannan fanni, bai dace a bukaci Sin ta shiga wata yarjejeniya makamancin wannan ba. Abun da Amurka ta kasa fahimta shi ne, a yunkurinta na matsawa kasar Sin da kokarin ci gabanta, tana kara mata kaimi da kwarjini a idon duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China