Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Har kullum kasar Sin na kasancewa mai aikatawa da kare ra'ayin cudanyar bangarori da dama
2020-10-07 16:51:39        cri

 

"Matsalolin da duniya ke fuskanta suna da yawa, kuma a yanzu kasashen duniya na kara fuskantar kalubale na bai daya. To sai dai kuma, za a iya warware su ne kawai ta hanyar tattaunawa da hadin kai. Ya kamata a daidaita al'amuran kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari, da ba da taimako ga juna, wanda hakan ya riga ya zama wani ra'ayin bai daya na kasashen duniya." Wadannan kalamai, wani sashe ne daga cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, a gun taron koli na cika shekaru 75 da kafa MDD, wanda aka shirya a kwanan baya.

Jawabin bidiyo da shugaba Xi Jinping ya gabatar ya samu karbuwa a tsakanin al'ummomin duniya, abin da ya nuna bukatar gaggawa, da muhimmancin amsa kalubalen da ke tattare da hadurran duniya a halin yanzu, bisa ra'ayin kasancewar bangarori da dama.

Tun farkon wannan shekarar, annobar numfashi ta COVID-19 da ta faru ba zato ba tsamani, ta yi mummunan tasiri ga zamantakewar dan Adam. Harkokin kasuwanci na yau da kullun na kasashe daban-daban duk sun tsaya, kuma tattalin arzikin duniya ya samu koma baya. A lokaci guda, daidaikun masu karfin fada a ji suna ci gaba da tafiya kan ra'ayin cin gashin kai, wadda hakan ke matukar illa ga hadin gwiwar kasa da kasa game da kandagarkin annobar da shawo kanta.

Kasar Sin ba ta taba tsayawa da kokarinta ba, wajen shawo kan kalubalen da annobar ta haifar, da inganta farfadowar tattalin arzikin duniya. Yanzu haka kuma, tana gaggauta kafa sabon tsarin ci gaba dake mayar da hankali kan raya tattalin arziki a cikin gida, tare kuma da hade kasuwar cikin gida da ta ketare. Wannan ba kawai domin biyan bukatun cikin gidanta na samun ci gaba mai inganci ba, har ma ya nuna ra'ayin kasar na bude kofar manyan kasuwanninta ga kasashen ketare, hakan ya nuna nauyin da ke kan kasar Sin a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Kasar Sin za ta ci gaba da samar da gudummawarta wajen warware matsalolin duniya, kuma a ko yaushe, tana zama mai kiyaye zaman lafiya a duniya, mai ba da gudummawa ga ci gaban duniya, da kuma kare tsarin kasa da kasa. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China