Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daga na gaba ake gane zurfin ruwa
2020-10-12 17:56:31        cri

Shugaba na gari har kullum ya kasance tamkar wata fitila ce dake haskawa al'umma hanya. Yayin da shugabannin suka kasance na gari masu cikakken burin gina kasa, da gina al'ummarsu, da son ci gaban jama'arsu, da kuma kokarin kyautata zaman rayuwar al'ummarsu, tabbas wadanann al'umma kakarsu ta yanke saka wato abin nufi sun taki sa'a.

Wani abin lura shi ne, salon kamun ludayin jagorancin shugaban kasar Sin na yanzu Xi Jinping, yana cike da muhimman darussa, musamman bisa la'akari da yadda a koda yaushe yake ikirarin gina al'ummarsa da samar da shugabanci na gari ta yadda a nan gaba sauran matasan dake tasowa za su kwaikwaiya domin dorawa daga inda aka tsaya. A lokuta da dama, shugaban ya sha nanata aniyarsa na burin mayar da rayuwar jama'a a gaban komai. Hakan ne ta sa shugaban yake yawan karfafawa matasan kasar Sin gwiwa domin su zama masu kishin al'umma, da jajurcewa, da tsayawa tsayin daka, domin ganin sun yiwa al'ummarsu hidima musamman a lokacin da suke kan ganiyar kuruciyarsu. Koda a karshen wannan mako, sai da shugaban ya yi kira da babbar murya ga matasa jami'an gwamnati da hukumomi na kasar da su kasance masu kokarin nuna juriya, da sadaukar da kai, inda ya bukaci su kara himma da kwazo wajen kokarin warware dukkan matsalolin da ake fuskanta na zahiri, ya kamata a sa kaimi, kuma a samar da hakikanin sakamako, in ji shugaban na Sin Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jami'iyyar kwaminis, kana shugaban kwamitin aikin sojin kasar, ya yi wannan kira ne a lokacin bude kwas din horas da matasan jami'ai da masu matsakaitan shekaru a kwalejin horas da 'yan jami'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC. A cewar shugaban, tarihi ya samu ci gaba ta hanyar warware matsaloli, Xi ya jaddada cewa, ta hanyar jagorantar al'umma don samar da juyin juya hali, da gina kasa, da sauye-sauye, kuma baki dayan manufar jami'iyyar CPC ita ce warware dukkan matsaloli na zahiri a cikin kasa. A cewar shugaban, a wannan hali da ake ciki mai cike da sarkakiya da rashin tabbas, da wahalar sha'ani, akwai bukatar gaggawa ga jami'ai su kara karfafa matakansu na warware matsaloli, ya kara da cewa, wannan wata bukata ce wacce ta zama tilas ga jami'ai matasa masu jini a jika dake da karancin shekaru domin su samu kwarin gwiwa.

Xi ya ce, jami'ai, musamman matasa, tilas ne su kara himma kan muhimman ayyukan al'umma dake bisa wuyansu, kuma su yi amfani da dukkan karfinsu wajen nazartar al'amurra, da zartar da hukunci bisa tsari, da hikima, da tunani mai cike da hangen nesa, da zurfafa yin gyare-gyare, da daukar matakai na gaggawa, da tattaunawa tare da jama'ar kasa, da kuma aiwatar da manufofi yadda ya kamata.

Ko shakka babu wannan burin shugaban Sin abin alheri ne kuma abin koyi, da ma dai masu hikimar magana sun ce; "daga na gaba ake gane zurfin ruwa". (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China