Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Salon rigakafin COVID-19 na gama gari yana tattare da kalubale
2020-10-13 10:48:43        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO怀Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce salon yiwa mafi yawa na al'ummar duniya allurar rigakafin cutar COVID-19, yana tattare da matsaloli da kalubale idan an kalle shi ta mahangar kimiyya.

Mr. Tedros wanda ya bayyana hakan, yayin taron menema labarai a jiya Litinin, ya ce ana amfani ne da salon yiwa al'umma mafiya rinjaye rigakafi domin ba su kariya daga wata cuta da aka riga aka fahimta.

Ya ce ga misali, ana bukatar yiwa kaso 95 bisa dari na al'ummar duniya allurar rigakafin kyanda, domin samar da kariya daga harbuwa daga cutar, wadda a irin wannan yanayi ake fatan ragowar kaso 5 da suka rage ba za su kamu da ita ba. Kaza lika a cewar jami'in, irin wannan salo yana ba da kariya ne ga mutane, ba wai ba su damar fuskantar cutar ba kariya ba. Kuma a tarihi ba a taba amfani da wannan salo wajen magance annobar da ta barke ba.

Da ya waiwayi batun cutar COVID-19, Mr. Tedros ya nanata cewa, har yanzu duniya ba ta da cikakkiyar masaniya game da dabarun kare jikin bil Adama daga harbuwa da ita. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China