Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tedros Adhanom Ghebreyesus: Matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen hana yaduwar COVID-19
2020-08-13 10:31:37        cri

Babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, matasa sun taka muhimmiyar rawa a kokarin da ake yi na hana yaduwar cutar. Duk da cewa galibin matasa ba sa fuskantar barazanar fama da cututtuka masu hadari sakamakon kamuwa da annobar COVID-19.

Jami'in ya bayyana haka ne, yayin bikin ranar matasa ta duniya na wannan shekara, wanda aka yiwa lakabi da " Shigar matasa yakin da duniya ke yi da wannan annoba". Babban darektan da takwaransa na UNESCO Audrey Azoulay, duk sun yabawa matasa, da kungiyoyin matasa da gamayyar matasa a sassa daban-daban na duniya, bisa rawar da suka taka a yaki da COVID-19.

Ya ce, annobar ta yi mummunan tasiri kan makomar matasa, ba kawai kwayar cutar ita kadai ba, amma saboda yadda cutar ta yi tasiri kan tattalin arziki, da ayyukan yi, da harkar ilimi da baki dayan tsarin kiwon lafiya.

A don haka ya yi kira ga matasa, da su gane su kuma yi zabin da ya dace game da lafiyarsu, ta yadda za su rayu tsawon shekaru cike da koshin lafiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China