Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta kafa wata tawagar kwararru kan kimiyyar halayya domin taimakawa yaki da COVID-19
2020-07-31 10:02:11        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da kafa wata tawagar kwararru mai ba da shawara kan kimiyya da ilimin hallayar dan Adam domin kiwon lafiya, a matsayin wani kokari da zai taimakawa yaki da annobar COVID-19.

Darakta Janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaidawa wani taron manema labarai da aka yi jiya ta kafar bidiyo cewa, tawagar za ta taimaka wajen fadadawa da zurfafa aikin da WHO ke yi kan kimiyyar hallaya, kuma za ta taimakawa ayyukan hukumar na bada shawarwarin kiwon lafiya mai karfi da inganci.

Tawagar ta kunshi kwararru 22 daga kasashe 16, wadanda ke da kwarewa a fannoni daban daban na hallayar dan Adam.

A cewarsa, tawagar za ta ba WHO shawara kan yadda za a kara, tare da inganta amfani da kimiyyar halayyar dan Adam a bangarorin lafiya daban daban, ciki har da COVID-19.

Ya kara da cewa, da taimakon sabuwar tawagar, WHO za ta samu damar taimakawa kasashe daukar matakan da suka fi dacewa na kare lafiyar al'umma. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China