Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Fasahohin kasar Sin"za su inganta aikin kiyaye muhallin duniya
2020-10-01 21:27:32        cri

A yayin taron koli na Majalisar Dinkin Duniya game da kiyaye nau'o'in halittu da aka gudanar jiya Alhamis 30 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda hudu kan yadda za a kiyaye nau'o'in halittu, da kuma more fasahohi guda uku da kasarsa ta samu a wannan fannin. Musamman ma yadda ya sake nanata burin kasar Sin na rage fitar da hayaki na Carbon Dioxide, da yin kira ga hadin kan kasa da kasa wajen kiyaye muhallin duniya bisa ra'ayin kasancewar bangarori da dama, matakin da nuna yadda babbar kasa dake sauke nauyin dake bisa kanta, da kuma inganta ayyukan kiyaye muhallin duniya baki daya.

 

 

Shugaba Xi Jinping ya kuma yi kira ga kasashe daban daban da su nace wajen kiyaye muhalli, da kara raya kyakkyawar duniya, da tsayawa kan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da hadin kan kasa da kasa don kiyaye muhallin duniya, kana da dagewa kan kokarin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da inganta ci gaban tattalin arziki bayan annoba. Baya ga haka,kowane bangare ya yi kokarin daukar nauyi dake bisa wuyansa, da kuma kara karfin aiwatar da shirin tinkarar kalubale da suka shafi kare muhalli.

 

 

Bisa shirin da aka yi, kasar Sin za ta shirya babban taro karo na 15 na bangarorin da suka cimma yarjejeniyar kiyaye nau'o'in halittu a shekara mai zuwa a birnin Kunming na kasar Sin. "A yayin da muke fuskantar kalubale a fannin muhalli, kasashe daban daban suna da makomar bai daya, ra'ayin bangare daya ba zai samu amincewa ba, hadin kai shi ne hanya daya kacal da ta dace." ra'ayin shugaba Xi Jinping ya dace da ra'ayin bai daya na dukkan kasashen duniya, ya kuma nuna muhimmancin daidaiton da ake fatan cimmawa a gun taron da za a shirya a shekara mai zuwa a Kunming. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China