Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Kasar Sin za ta taka rawa kan kiyaye muhallin duniya baki daya
2020-10-01 17:56:24        cri

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi ta kafar bidiyo a taron koli na Majalisar Dinkin Duniya game da kiyaye nau'o'in halittu a ranar 30 ga watan Satumba, inda ya ba da shawara ga kasashe daban daban da su tsaya kan kiyaye muhalli, da hadin gwiwar bangarori da dama, da samun ci gaba tare da kiyaye muhalli, da kara daukar nauyin dake bisa wuyansu, kana ya jaddada cewa, kasarsa zata ci gaba da bin manufar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, da kara taka rawa kan kiyaye nau'o'in halittu masu dinbin yawa da kiyaye muhallin duniya.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, a wannan lokacin na cika shekaru 75 da kafuwar MDD, kuma lokaci ne na musamman da kasashe daban daban ke kokarin yaki da cutar COVID-19, da inganta farfadowar tattalin arziki mai inganci, MDD ta shirya taron koli na kiyaye nau'o'in halittu masu dimbin yawa, domin tattauna manyan batutuwan da suka shafi kiyaye halittu iri daban daban da inganta neman dauwamamman ci gaba, lallai wannan yana da ma'ana kwarai da gaske.

Game da haka, shugaba Xi Jinping ya kuma gabatar da shawarwari guda hudu: "Da farko, a tsaya kan kiyaye muhalli, da karfafa raya kyakkyawar duniya. Na biyu, a tsaya kan ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da hada kan kasa da kasa don kiyaye muhallin duniya. Na uku, a dage kan kokarin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da inganta ci gaban tattalin arziki bayan annobar. Na hudu, a kara daukar nauyi dake bisa wuyan kowane bangare, da kuma kara karfin aiwatar da shirin tinkarar kalubale daga fannin kare muhalli."

Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasancewar nau'o'in halittu masu dimbin yawa, muhimmin tushe ne na rayuwar dan Adam da ci gabansa. A yayin da ake neman ci gaba, kamata ya yi a dora muhimmanci kan kiyaye halittu.

Baya ga haka, Xi Jinping ya nuna cewa, "A yayin da muke fuskantar kalubale a fannin muhalli, kasashe daban daban suna da makomar bai daya. Ya kamata mu tsaya kan kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin manufar MDD, da martaba dokokin kasa da kasa, da kuma kara kaimi wajen kiyaye muhallin duniya. Kana ya kamata mu sa himma wajen sauke nauyin da ke bisa wuyanmu, da cika alkawurran da muka dauka, da tabbatar da burin da muke son cimmawa, don hana bacewar nau'o'in halittu daga doron kasa."

Shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana bin manufar kiyaye muhalli wajen jagorantar ci gaba, da mayar da aikin kiyaye muhalli a wani matsayi mai muhimmanci. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana sa himma a harkokin kula da muhallin duniya, da cika alkawurran da ta yi wadanda suka shafi sauyin yanayi, halittu daban-daban da sauran yarjejeniyoyin kare muhalli, har ma kasar ta kammala burin magance sauyin yanayi da kafa yankunan kiyaye halittu na shekarar 2020 kafin lokacin da aka tsara.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, "Kasar Sin zata bi manufar raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil Adama, don kara bayar da gudummawa bisa radin kanta, da aiwatar da manufofi da matakai masu karfi, don kara ba da himma da gudummawa wajen cimma burin da aka tsara karkashin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China