Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan kungiyoyin al'ummun kasar Sin sun gabatar da jawabai a taron hukumar kare hakkin dan-Adam na MDD
2020-10-01 16:25:55        cri
A kwanakin baya ne, wakilan kungiyoyin al'ummmomin na kasar Sin sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo, yayin taron hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD karo na 45 da aka gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland, domin bayyana ra'ayin kasar Sin

Karkashin batutuwan da abin ya shafa game da 'yancin samun bunkasuwa, wakilin kungiyar musaya ta kasa da kasa ta kasar Sin, ya bayyana cewa, 'yancin yin rayuwa da samun bunkasuwa, su ne jigon hakkin bil-Adama. A don haka, "muna fatan ganin dukkan kasashe sun samu 'yancin bunkasuwa ta hanyar yin shawarwari da juna, da mutunta 'yancin zabin da al'ummun sauran kasashe suka yi na samun bunkasuwa, da nuna adawa da yadda wasu kasashe ke tilastawa sauran kasashe hanyarsu ta raya kasa, da yin adawa da yadda wasu daidaikun kasashe ke muzanta wasu kasashe saboda wasu muradunsu, tare kuma da yin kira ga dukkan bangarori, da su karfafa yin tattaunawa, da yin musaya da hadin gwiwa da bunkasa hanyoyin samun ci gaba mai dorewa.

A jawabinsa, wakilin gidauniyar yaki da talauci na kasar Sin, ya bayyana cewa, ci gaba wani take ne na al'umma, kana kawar da duk wani nau'in talauci, yana daya daga cikin muhimman hanyoyin bunkasa da tabbatar da 'yancin samun bunkasuwa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China