Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afirka ya kai kusan miliyan 1 da dubu 400
2020-09-21 10:44:13        cri

Hukumar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC), ta sanar da cewa, ya zuwa jiya Lahadi, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar ya kai 1,399,186, kana yawan mutanen da cutar ta halaka ya kai mutane 33,818.

Hukumar ta ce, ya zuwa yanzu, yawan mutanen da aka tabbatar sun warke daga cutar a sassan nahiyar ya kai 1,148,578. Sai dai kasashen nahiyar sun fuskanci mabanbantan tasirin cutar. Kasashen nahiyar da cutar ta fi shafa a cewar Africa CDC, sun hada da Afirka ta kudu, da Masar, da Morocco, da Habasha da kuma Najeriya.

Rahotanni na cewa, a cikin makon da ya gabata, kasar Morocco ce, ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar, inda cutar ta harbi mutane 14,603, sai Afirka ta kudu mai mutane 11,013, yayin da cutar da harbi mutane 4,742 a kasar Habasha.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China