Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudin harajin da ma'aikatar harkokin kudi ta Najeriya ta samu ya ragu da kashi 60 cikin dari
2020-09-28 13:41:21        cri
A ranar Asabar ne mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce, yawan kudin harajin da ma'aikatar harkokin kudin kasar ta tara ya ragu da kashi 60 cikin dari, kuma gwamnatin kasar ba za ta iya ci gaba da biyan kudin tallafin man fetur ba, don haka ba zai yiwu gwamnatin ta hana karuwar farashin fetur ba.

Jaridar THISDAY ta Najeriya ta rawaito mataimakin shugaban Najeriyar na cewa, a halin yanzu gwamnatin kasar tana kokarin neman sabuwar hanya ta maye gurbin tsarin biyan tallafin man fetur tare da daidaita matsalar.

Osinbajo ya yi nuni da cewa, a mataki na gaba, gwamnatin kasar za ta kara maida hankali kan samar da iskar gas ta Compressed Natural Gas, wanda farashinta ke kan Naira 70 zuwa 80 a kowace lita. Ya ce idan ake kai ga fara amfani da wannan sabon makamashi a motocin sufurin jama'a, hakan zai sassauta illar da za a fuskanta a kasar, a sakamakon soke bada tallafin man fetur. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China