Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan BH 13 sun mika wuya ga dakarun Najeriya
2020-09-28 09:51:53        cri
Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa, wasu mutane 13 da ake zargin mayakan BH ne, sun mika wuya ga dakarunta yayin wani aikin zakulo ragowar mayakan kungiyar dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwar da kakakin rundunar John Enenche ya fitar, ta ce mayakan sun mika wuya ne a ranar Asabar, yayin da sojojin suka kai hare-hare ta sama da nufin fatattakarsu a yankin Bama dake arewacin jihar Borno.

A cewar John Enenche, yara 17 da mata 6 da aka tabbatar iyalai ne na mayakan, su ma sun mika wuya ga dakarun a kauyen Kodila dake yankin na Bama.

Ya kara da cewa, yanzu haka, ana bincike da tantance mayakan da suka mika wuya, kamar yadda ka'idojin irin aikin na duniya ya tanada.

Tun cikin shekarar 2009, kungiyar BH ke fafutukar kafa daular Islama a arewa maso gabashin Nijeriya, inda hare-harensu ya ketara zuwa kasashen yankin Tafkin Chadi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China