Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana son ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a kasar Mali
2020-09-28 20:53:06        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau Litinin cewa, an yi bikin rantsar da shugaban rikon-kwarya na Mali Bah Ndaw, wani muhimmin mataki a yunkurin da ake na mika mulki a kasar.

Wang ya ce, kasar Sin tana mutunta Mali na zabar hanyar raya kasarta bisa radin kanta, kuma tana fatan ci gaba da kokari tare da bangarori masu ruwa da tsaki a kasar, domin tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a kasar. A matsayinta ta babbar kawar Mali, Sin na son kara kokari tare da sauran kasashen duniya domin bada gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da ci gaba a Mali.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China