Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi kira da a warware rikicin Mali ta hanyar lumana
2020-08-19 19:24:36        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki a kasar Mali, da su yi kokarin kare muradun kasar da jama'arta su kuma warware bambance-bambancen dake tsakaninsu cikin lumana ta hanyar tattaunawa.

Zhao ya bayyana haka ne, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa a lokacin da aka tambaye shi game da murabus din da shugaban kasar ta Mali Ibrahim Boubacar Keita ya yi, wanda a halin yanzu yake hannun sojojin da suka yi bore.

Ya ce, kasar Sin tana bibiyar halin da ake ciki a kasar Mali, tana kuma adawa da sauya mulki ta hanyar da ba ta dace ba, kamar amfani da karfin tuwo. Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kokarin da kungiyoyin shiyya da na kasa da kasa, musamman kungiyar tarayyar Afirka(AU) da ECOWAS, suke yi wajen lalubo bakin zaren warware rikicin kasar cikin lumana.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China