Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa 413 sun tafi Mali aikin wanzar da zaman lafiya
2019-05-15 11:21:28        cri
Kimanin Sinawa 413 ne a ranar Talata suka tashi daga Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar, zuwa kasar Mali dake yammacin Afrika domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na MDD na tsawon shekara guda.

Jami'an wanzar da zaman lafiyar, sun hada da jami'an tsaro 210, da injiniyoyi 140, da kuma bangaren jami'an kiwon lafiya 63, su ne tawaga ta 7 da aka tura zuwa kasar.

Jami'an za su gudanar da ayyuka masu yawa, da suka hada da samar da tsaro, da ayyukan kiwon lafiya, da kuma gina hanyoyin mota da filin jirgin sama.

Kafin tafiyar jami'an sun halarci wani horo na musamman domin samun dabarun kariya daga hare haren ta'addanci da kaucewa tarzoma, da jurewa tsananin zafi a yankin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China