Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai muhimmancin gina jihar Xinjiang bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamani
2020-09-27 16:15:41        cri

Kwamitin tsakiya na JKS ya kira taron tattaunawa kan ayyukan da suka jibanci jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin karo na uku a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar tsakanin ranar 25 zuwa 26 ga wata, inda babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Xi Jinping ya jaddada cewa, akwai muhimmancin gina jihar Xinjiang bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamani. Ma'anar gina jihar bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin ita ce, gwamnatin jihar tana tafiyar da harkokin jihar bisa doka karkashin jagorancin kwamitin JKS, tare da samun halartar daukacin al'ummun jihar, ta yadda za a samar da tsarin ginawa tare da kulawa tare da kuma morewa tare a jihar.

Duk da cewa an samu babban sakamakon da ba a taba ganin irinsa ba a baya a bangarorin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kyautatuwar rayuwar al'umma a jihar ta Xinjiang bayan kokarin da aka yi, kuma al'ummun jihar 'yan kabilu daban daban suna kara jin dadin rayuwarsu, amma idan ana son tabbatar da ci gaba mai dorewa a jihar, to ya dace a yi kokarin gina jihar Xinjiang bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, inda al'ummun jihar suke zaman jituwa tare, kuma suke samun wadata, da ci gaban wayewar kai ba tare da gurbata muhalli ba, dalilin da ya sa haka shi ne, babban burin gudanar da ayyukan da suka jibanci jihar shi ne, domin tafiyar da harkokin jihar bisa doka, ta yadda za a ciyar da jihar gaba cikin lumana.

Shugaba Xi, ya bayyana cewa, idan ana son tabbatar da kwanciyar hankali mai dorewa a jihar Xinjiang, ya kamata a tafiyar da harkokin jihar bisa doka daga duk fannoni karkashin jagorancin JKS bisa tsarin gurguzu.

Hakika tun asali 'yan kabilu daban daban suna zaman rayuwa tare a jihar Xinjiang, a don haka ya dace a kara karfafa hada kai tsakaninsu ta hanyar kara karfafa cudanyar dake tsakaninsu, domin gina kyakkyawar makomar al'ummun kasar Sin baki daya.

Kamar yadda shugaba Xi ya yi tsokaci, babban burin aikin JKS shi ne, tabbatar da dadin rayuwa ga daukacin al'ummun kasar Sin, wadanda ke hada al'ummun 'yan kabilu daban daban na jihar Xinjiang, tare kuma da fardado da al'ummun kasar, shi ya sa akwai bukatar a gina jihar Xinjiang bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki, kuma muradun nan yana da ma'ana matuka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China