Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yabanya mai armashi da kasar Sin ta samu na shaida ikon kasar na samar da isasshen abinci
2020-09-22 21:39:22        cri

Yau Talata 22 ga watan Satumba, rana ce ta bikin manoman kasar Sin. Alkaluman baya bayan nan a fannin noma, sun nuna yadda aka noma karin hatsi a filayen noma a wannan kaka. Hakan dai na nuni da cewa, Sin ta samu daidaito a fannin ayyukan gona, kana ta samu isasshiyar yabanya, da tabbacin wadatar abinci.

Tun farkon wannan shekara, an fuskanci kalubale da dama, ciki hadda bullar cutar COVID-19, da ambaliyar ruwa mai tsanani a kogin Yangtze, wadanda suka haifar da kalubale ga fannin noma na kasar Sin.

A mataki na kasa da kasa kuwa, annobar COVID-19, da yaduwar farin dango, sun sanya MDD yin hasashen aukuwar fari a kasashe a kalla 25 a wannan shekara da muke ciki. Game da hakan ne kuma, ake ganin cewa Sin ta yi namijin kokari wajen cimma nasarar da ta samu, wanda kuma hakan zai yi tasiri ga samuwar isasshen abinci a duniya.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, adadin abincin da al'ummun kasar Sin ke amfani da shi a shekara, ya kai kilogiram 470, wanda ya haura adadin da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai wato kilogirma 400 ga ko wane mutum. Kaza lika yanayin wadatar abinci a kasar na kara kyautata. Daya daga muhimman dalilai da suka haifar da hakan kuwa shi ne, gwamnatin Sin na dora muhimmancin gaske, ga batun samar da isasshen hatsi cikin dogon lokaci.

A hannu guda kuma, Sin ta fitar da tsare tsaren raba dabarun ta, da kwarewar ta a fannin wanzar da wadatar abinci, tana kuma shiga a dama da ita, a harkokin gudanarwa na samar da isasshen abinci. Bugu da kari, tana bayar da tallafin gaggawa na abinci gwargwadon iyawar ta. Matakin dake nuni ga irin nauyin da ta sauke, a matsayin ta na babbar kasa a wannan fanni.

Ko da a ranar 17 ga watan nan ma, sai da Sin ta samar da tallafin abinci na gaggawa ga kasar Sudan ta kudu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China