Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jita-jita ba za ta zama gaskiya ba
2020-09-26 15:26:14        cri

A jiya Juma'a ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Wenbin, ya yi wani jawabi a wajen wani taron manema labarun ma'aikatarsa, inda ya karyata rahoton da wata cibiyar nazarin manyan tsare-tsare ta kasar Australiya ta gabatar, wanda ya ce wai hukumar jihar Xinjiang ta kasar Sin ta rushe masallatai da dama.

Wang ya ce, wannan cibiyar nazari ta kasar Australiya, kullum tana karbar kudi, tana yada jita-jita game da kasar Sin, don haka ba ta da imani ko kadan. Sa'an nan wannan rahoton da ta gabatar a wannan karo karairayi ne tsantsa. A cewar wannan jami'i, ana tabbatar da ingancin 'yancin addini, da hakkin dan Adam sosai a jihar Xinjiang ta kasar Sin, ana kuma kokarin kare hakki da 'yanci na al'ummomi daban daban dake jihar, ciki har da 'yan kabilar Uygur.

Jami'in ya dauki yawan masallatan dake jihar Xinjiang a matsayin wani misali, ya ce, akwai kimanin masallatai dubu 24 a jihar. Wannan adadi ya nuna cewa, kusan duk Musulmai 530 na da masallaci guda domin yin ibadar su. Kana yawan masallatai a jihar Xinjiang ya ninka jimilar wadanda ke akwai a daukacin kasar Amurka da ninki goma. Yayin da yawan masallatai da mutanen jihar Xinjiang ke da su, suka haura na wasu kasashen Musulmi.

Ban da wannan kuma, game da wasu adireshin da cibiyar nazarin manyan tsare-tsare ta kasar Australiya ta fitar, cewa wai sansanoni ne na kulle 'yan kabilar Uygur, wasu kwararru sun yi bincike a kan adireshin, tare da gano cewa, wasunsu yankuna ne na raya masana'antun samar da kayayyakin lantarki, har ma daya daga cikinsu unguwa ce ta jama'a mai inganci. Don haka, jami'in ya ce, wannan rahoton da aka gabatar, babu gaskiya a ciki, kawai jita-jita ce da ake yada don neman shafawa kasar Sin kashin kaji.

Sai dai duk da haka, irin wadannan jita-jita, cewa wai gwamnatin kasar Sin na musgunawa Musulmai, na yaduwa sosai a shafukan yanar gizo na Internet, gami da kafofin watsa labaru. Don haka, mutane da yawa, musamman ma wadanda ba su san kasar Sin sosai ba, su kan yi kuskure wajen amincewa da jita-jitar da ake kokarin yadawa.

Game da wadannan mutane, ya kamata su fahimci cewa, a matsayin wata babbar kasa mai bin tsarin siyasa na gurguzu, kasar Sin tana da wasu makiya a duniya. Musamman ma wasu kasashen dake yammacin duniya, wadanda suke kallon tasowar kasar Sin a matsayin wata barazana gare su. Don haka suna ta kokarin yada jita-jita game da kasar Sin, don neman janyo kiyayya kan kasar, da yin amfani da hanyoyi daban daban don hana kasar samun ci gaba cikin sauri.

Wani lokaci ma, jita-jitar na samun yaduwa sosai, har ma tana iya shiga kunnuwanka, ta bakin wasu shahararrun mutane, ko kuma manyan kafofin watsa labarai, da abokan ku. Duk da haka, jita-jita ba gaskiya ce ba. Kamar yadda Hausawa kan ce, kome nisan jifa, kasa zai fado. A karshe za a san halayyar kasar Sin, da yadda take daukaka 'yancin bin Addini, da kaunar jama'ar kasar masu bin Musulunci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China