Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni kimanin 1400 sun halarci bikin bajekolin littattafai na Beijing
2020-09-27 15:32:35        cri
An kaddamar da bikin bajekolin littattafai na birnin Beijing karo na 27 jiya, ta kafar yanar gizo ta Internet. Hakan ya kasance karo na fako, da aka gudanar da wannan biki, da tarihinsa ya kai shekaru 34, ta kafar yanar gizo wato Internet.

Duk da cewa an canza tsarin bikin a wanna karo, amma yawan masu halartar bikin ba su ragu ba, idan an kwatanta da na baya. Zuwa ranar 25 ga wata, wasu kamfanoni kimanin 1400, na wasu kasashe da yankuna 97, sun riga sun yi rajista don halartar bikin, tare da gabatar da littattafai fiye da dubu 38. Cikin wadannan kamfanoni, akwai wasu 200 da suke halartar bikin a karon farko, kana rabi daga cikin manyan kamfanoni masu tsara littattafai 50 a duniya sun halarci bikin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China