Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana wajen wani taron karawa juna sani, dangane da batun jihar Xinjiang, cewa don tabbatar da samun kwanciyar hankali mai dorewa a jihar Xinjiang, ya kamata a tabbatar da gudanar da ayyukan mulki bisa doka, yayin da ake kula da fannonin jihar daban daban, ta yadda za a samar da wani tsarin kula da al'umma, na sanya bangarori daban daban yin aikin kulawa tare, da cin more tare.
Xi ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa hadin kan al'ummun kasar Sin, da ba su cikakkun damammakin musayar ra'ayi, da mu'amala da juna. (Bello Wang)