Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi hadin gwiwa da hukumomin MDD wajen shirya taron rage talauci
2020-09-27 10:54:23        cri
A jiya Asabar, kasar Sin, da sashen kula da aikin raya tattalin arziki da zaman al'umma na MDD, da hukumar shirin raya kasa ta Majalisar, sun yi hadin gwiwa, wajen shirya wani taron manyan kusoshi na tattauna batun rage talauci, da hadin gwiwa tsakanin kasashen masu tasowa, ta kafar bidiyon. Inda mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi ya jagoranci taron, tare da ba da jawabi.

Wang ya ce, a wannan lokacin da kasashe daban daban ke fuskantar matsin lamba a fannonin tinkarar annoba, da kokarin kare tattalin arziki, da zaman rayuwar jama'a, ya kamata kasashe masu tasowa su kara kokarin hadin gwiwa da juna, don neman samun ci gaba tare.

Wang ya ba da shawarwari a fannoni guda 4, wadanda suka hada da daukaka ajandar neman samun cigaba mai dorewa nan da shekarar 2030, da neman cimma buri na kawar da talauci tare, da neman ganin bayan cutar COVID-19, gami da karfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China