2020-09-14 21:10:51 cri |
Yau kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, labaran dake shafar yankin Xinjiang na kasar Sin da aka wallafa a kan shafin yanar gizon ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka jita-jita ce kawai ake bazawa.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, adadin al'ummun 'yan kabilar Uygur dake yankin Xinjiang ya karu daga miliyan 5.55 zuwa miliyan 12 a halin yanzu, kana adadin masallatai dake yankin ya kai kusan dubu 24, adadin ya kai ninka na kasar Amurka sau goma, ban da haka har kullum ana kare hakkin 'yan kananan kabilun dake yankin Xinjiang, bisa dokokin aiki da na kwangila, amma ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi watsi da duk wadannan hakikanin abubuwa, tana shafawa yanayin kare hakkin dan Adam da yankin ke ciki bakin fenti kamar yadda take so.
Wang Wenbin ya kara da cewa, makasudin Amurka shi ne domin gurgunta wadata da kwanciyar hankali na yankin Xinjiang ta hanyar fakewa da batun hakkin dan Adam, kana tana son hana ci gaban kasar Sin.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China