Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ya dace a shimfida adalci tsakanin kasa da kasa a fannonin hakkoki da ka'ida
2020-09-23 09:53:54        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, annobar COVID-19 ba kawai jarabta kwarewar kasa da kasa wajen tafiyar da harkokin mulki kawai take yi ba, har ma tana jarabta tsarin tafiyar da harkokin duniya baki daya.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, a jawabin da ya gabatar yayin muhawarar babban taron MDD karo na 75 wanda aka yi jiya Talata ta kafar dibiyo.

Ya ce, ya kamata a martaba ra'ayin cudanyar bangarori daban-daban, da kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD. Yana mai cewa, ya zama dole kasa da kasa su kara yin shawarwari da more damammaki tare a yayin da ake tafiyar da harkokin duniya, da shimfida adalci a fannonin da suka shafi kare hakki da samar da zarafi da kuma kafa ka'idoji, ta yadda za'a samu ci gaba cikin lumana da karfafa hadin-gwiwa da cin moriyar juna tare.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China