Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Sin ta shiga hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da cuta COVID-19
2020-09-23 09:41:46        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a yayin muhawarar babban taron MDD karo na 75 a jiya Talata, inda ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da raba fasahohin yaki da cutar COVID-19 da bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar, da samar da goyon baya da gudummawa ga kasashe masu bukatar taimako, da tabbatar da samar da kayayyakin yaki da cutar COVID-19 a duniya, tare da shiga nazarin gano asalin kwayoyin cutar da hanyoyin yaduwarta. Ya ce, yanzu haka alluran rigakafin cutar da dama da kasar Sin ke kokarin samarwa, sun shiga matakin gwaji na uku, kuma da zarar an gama yin nazarin, duniya baki daya za ta ci gajiyarsu, kuma za a bada fifiko musamman ga kasashe masu tasowa. Sin za ta yi kokarin cika alkawarinta na samar da gudummawar dala biliyan 2 don zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannonin aikin noma, da yaki da talauci, da bada ilmi, da harkokin mata da yara, da tinkarar matsalar sauyin yanayi da sauransu don taimakawa kasashe farfado da tattalin arzikinsu da inganta rayuwar al'umma. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China