Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin habaka sassan ilimi da al'adu da lafiya da wasanni
2020-09-22 20:55:32        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin bunkasa sha'anin ilimi da raya al'adu, da kiwon lafiya da kuma wasanni a kasarsa. Shugaban ya ce wadannan sassa na da tasiri a fannin karfafa gamsuwar rayuwa, da samar da farin ciki da tsaro.

Xi ya yi kiran ne a Talatar nan, yayin taron karawa juna sani da ya jagoranta, wanda kuma ya samu halartar wakilai daga wadannan sassa.

Taron dai ya samar da damar jin ta bakin mahalarta, game da shirin tsara dabarun ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 14, wanda kasar ta Sin za ta aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China