2020-09-22 11:13:59 cri |
Tsohon ministan tsaro, kuma tsohon kanal din soja mai ritaya Bah N'Daw, ya zama shugaban kasar Mali na rikon kwarya bayan wata hukuma mai mambobi 17 da kwamitin kwatar 'yancin Mali, CNSP ya kafa ta zabe shi a ranar Litinin, shugaban kwamitin CNSP Assimi Goita shi ne ya sanar da hakan a jawabin da ya gabatarwa 'yan kasar ta gidan talabijin.
Matakin nadin shugaban kasar na rikon kwarya tare da mataimakinsa ya zo ne bayan tattaunawar da aka gudanar karkashin hukuma ta musamman wanda 7 daga cikin mambobinta 17 sun fito ne daga kwamitin CNSP, in ji Goita, ya kara da cewa, an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban kasar.
Goita ya ce, za a gudanar da bikin rantsar da shugaban rikon kwarya da mataimakinsa a ranar 25 ga watan Satumba.
Daga watan Mayun shekarar 2014 zuwa watan Janairun 2015, N'Daw ya zama ministan tsaron kasar Mali karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita, inda daga bisani ya yi murabus a ranar 18 ga watan Ogustan wannan shekarar bayan juyin mulkin da sojojin suka shirya.
A bisa ga kundin tsarin dokar gwamnatin rikon kwarya, wanda aka amince da shi a ranar 12 ga watan Satumba, wanda ta samu mahalarta kimanin 500 daga bangarorin kasar daban daban bayan shafe tsawon kwanaki uku suna tattaunawa, daga karshe sun cimma matsaya cewa, shugaban kasar na rikon kwarya da za a zaba zai iya kasancewa soja ko kuma farar hula, kuma gwamnatin rikon kwarya za ta shafe wa'adin watanni 18 ne don mika mulki ga sabuwar zababbiyar gwamnatin kasar.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China